Phil collins
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
FARKON RAYUWA
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a ingila inda a gidansu su hudu ne kuma shine dan auta[1] [2]
tun yana dan shekara 5[3] ya fara kidan ganga kuma yana dan shekara sha biyu auntyn shi ta koya mashi kada piano da da waka[4]
yayi firamare har ya kai shekara sha daya inda ya wuce makarantar koyon nahawu
Aikin shi
[gyara sashe | gyara masomin]ya bar makaranta lokacin yana dan shekara sha hudu inda ya fito a wasu fina finai kamar su A HARD DAY`S NIGHT
son waka ya kara shiga rayuwar shi inda ya samu aiki a wajen wasu masu waka inda suka zagaye kasar tare da shi
a shekarar 1970 ya zama mai kada ganga a cikin cikin mawaka masu suna genesis daga baya kuma ya zama shine babban mawakin su
a cikin shekarar 1984 yaci gaba da wakar shi shi kadai yayi wakoki kamar haka one more night/against all odds, take me home da sauran su
ya saki album din shi na wakoki fiye da shidda
ya samu kyauta a America a 1985 ya samu grammy awards har sau 3
bayan waka ya fito fina finai kala kala kamar su frauds,jugle book,the three bears da sauransu
Rayuwar shi
[gyara sashe | gyara masomin]yayi aure har sau ukku kuma ya sake su ya auri Andrea Bertorelli sun haifi da daya[5]
a 1994 ya auri Jill Tavelman suna da diya daya da ita wadda ta zama yar wasa[6]
a 1999 ya auri Orianne Cevey sun haifi yaya biyu tare da shi[7]
A 2012 ance shine na biyu da yafi kowa kudi a cikin masu kida na duniya
a 1999 ya dan samu matsalar rashin ji a kunnen shi na hagu bayan shekara 2 kuma ya warke [8]
an karrama shi da digiri da yawa saboda aikin da yake yi [9]