[go: nahoru, domu]

Jump to content

Unlimited L.A

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Unlimited L.A
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 2 ga Afirilu, 1987 (37 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a darakta, colorist (en) Fassara, edita da Mai daukar hotor shirin fim
Unlimited L.A

Buari Olalekan Oluwasegun' (an haife shi 2 Afrilu 1987; wanda aka fi sani da Unlimited LA) darektan bidiyon waka ne a Najeriya. Ya yi aiki tare da nau'ikan kiɗa da masu fasaha da yawa waɗanda suka haɗa da Olamide, Phyno, Timaya, da sauran su.

Tun daga shekarar 2011, ya yi aiki ga mawakan kida da yawa wajen ba da umarni na faifan wakokin su, musamman Olamide. A cikin 2015, ya sami Mafi kyawun Darakta a Kyautar Nishaɗi ta Najeriya ta 2015, kuma ya sami Mafi kyawun Bidiyo na Kiɗa a The Headies 2015, kuma ya sami nadi a All Africa Music Awards. A cikin 2016, an zabe shi a The Headies 2016 da 2016 Nigeria Entertainment Awards for Best Music Video. A cikin 2017, ya sami Mafi kyawun Darakta na shekara a Kyautar City People Entertainment.[1] [2]